Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

1 Peter 3 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 Likewise, wives, submit to your own husbands, so that even if some disobey the word, they may be won without a word by their wives' conduct, Haka ma, ku matan aure, ku yi biyayya ga mazanku, domin in waɗansunsu ba su gaskata maganar ba, wataƙila a shawo kansu ba tare da magana ba
2 seeing your pure, reverent conduct. sa’ad da suka ga rayuwarku mai tsabta da kuma na ladabi.
3 Do not let your beauty be the outward kind—braided hair, gold jewelry, fine clothing. Kyanku bai kamata yă zama na adon jiki ba, kamar kitso da sa kayan ado na zinariya da kuma sa kaya masu tsada.
4 But let it be the hidden person of the heart, the undying beauty of a gentle, quiet spirit, precious in our Father's sight. Maimakon haka, kyanku ya kamata yă zama ainihi na halinku na ciki, kyan da ba ya koɗewa na tawali’u da kuma na natsattsen ruhu, wanda yake mai daraja a gaban Allah.
5 For this is how the holy women of old who hoped in our Father adorned themselves, submitting to their own husbands, Gama haka matan masu tsarki na dā waɗanda suka sa begensu ga Allah suka yi wa kansu ado. Sun yi wa mazansu biyayya,
6 as Sarah obeyed Abraham, calling him lord. And you have become her children if you do good, fearing no terror. kamar Saratu, wadda ta yi biyayya ga Ibrahim, har ta kira shi maigidanta. Ku ’ya’yanta ne mata in kun aikata abin da yake daidai, ba ku kuma ba tsoro dama ba.
7 Husbands, similarly, live with your wives with understanding, honoring each as the weaker vessel and as coheirs of the grace of life, so your prayers aren't hindered. Mazan aure, ku ma, ku yi zaman sanin ya kamata yayinda kuke zama da matanku, ku girmama su a matsayin abokan zama marasa ƙarfi da kuma a matsayin magādan kyautar rai na alheri tare da ku, don kada wani abu yă hana addu’o’inku.
8 Finally, all of you, be of one mind, sympathetic, loving one another as family, tenderhearted, and humble. A ƙarshe, dukanku ku zauna lafiya da juna; ku zama masu juyayi, kuna ƙaunar juna kamar ’yan’uwa, ku zama masu tausayi da kuma tawali’u.
9 Do not repay evil for evil or insult for insult, but bless instead—you were called to this, so you may inherit blessing. Kada ku rama mugunta da mugunta ko zagi da zagi, sai dai ku sa albarka, gama ga wannan ne aka kira ku, ku kuma gāji albarka.
10 For, "Whoever desires to love life and to see good days, let him keep his tongue from evil and his lips from speaking deceit. Gama, “Duk wanda yake so yă ji daɗin rayuwa, yă kuma ga kwanaki masu kyau dole yă ƙame harshensa daga mugunta leɓunansa kuma daga maganar yaudara.
11 Let him turn away from evil and do good; let him seek peace and pursue it. Dole yă juye daga mugunta, ya aikata nagarta; dole yă nemi salama yă kuma bi ta.
12 For the eyes of our Lord are on the righteous, and his ears are open to their prayer, but the face of our Lord is against those who do evil." Gama idanun Ubangiji suna a kan masu adalci kunnuwansa kuma suna jin addu’arsu, amma fuskar Ubangiji tana gāba da masu mugunta.”
13 Now who is there to harm you if you are eager to do what is good? Wa zai yi muku lahani in kun himmantu ga yin nagarta?
14 But if you suffer for righteousness, you are blessed. Don't fear their fear, don't be shaken. Amma ko da za ku sha wahala saboda abin da yake daidai, ku masu albarka ne. “Kada ku ji tsoron abin da suke tsoro; kada kuma ku firgita.”
15 Set Christ apart as Lord in your hearts. Always be ready to answer anyone who asks the reason for your hope, but with gentleness and respect. Sai dai a cikin zukatanku ku keɓe Kiristi a matsayin Ubangiji. A kullum, ku kasance a shirye ku ba da amsa ga duk wanda yake neman ku ba da dalilin wannan begen da kuke da shi. Amma ku yi wannan cikin tawali’u da ladabi,
16 Keep a clear conscience, so that when you're slandered, those who insult your good conduct in Christ are shamed. tare da lamiri mai kyau, saboda waɗanda suke maganganun banza a kan kyawawan ayyukanku cikin Kiristi su ji kunya da irin ɓata suna da suke yi.
17 Better to suffer for doing good, if that's our Father's will, than for doing evil. Ya fi kyau, in nufin Allah ne, a sha wahala don yin nagarta fiye da yin mugunta.
18 For Christ too suffered once for sins, the righteous for the unrighteous, to bring us to our Father—put to death in flesh, made alive in spirit, Gama Kiristi ya mutu domin zunubi sau ɗaya tak, mai adalci saboda marasa adalci, don yă kawo ku ga Allah. An kashe shi a cikin jiki, amma an rayar da shi a Ruhu,
19 in which he also went and proclaimed to the spirits in prison, ta wurin wanda kuma ya tafi ya yi wa ruhohin da suke a kurkuku wa’azi
20 who disobeyed long ago, when our Father waited patiently in Noah's days as the ark was being built, in which a few—eight people—were brought safely through the water. waɗanda dā ba su yi biyayya ba sa’ad da Allah ya jira da haƙuri a kwanaki Nuhu yayinda ake sassaƙa jirgi. A cikinsa mutane kima ne kawai, su takwas, aka kuɓutar ta ruwa,
21 This corresponding baptism now saves you too—not removing body dirt, but appealing to our Father for a good conscience—through Jesus Christ's resurrection, ruwan nan kuwa kwatancin baftisma ne da yanzu ya cece ku ku ma, ba kawar da dauda daga jiki ba, sai dai yin alkawari na lamiri mai kyau ga Allah. Ya cece ku ta wurin tashin Yesu Kiristi daga matattu,
22 who entered heaven and is at our Father's right hand, with angels, authorities, and powers subject to him. wanda ya tafi sama, yana kuma a hannun dama na Allah, mala’iku, mulkoki da kuma masu iko suna masa biyayya.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]