Skip to content
The Believer's Library

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020

1 John 2 OHCB

Show OHCB only
Verse × ×
1 My dear children, I write this so you won't sin. But if anyone does sin, we have an advocate before the Father—Jesus Christ, the righteous one. ’Ya’yana ƙaunatattu, ina rubuta muku wannan ne don kada ku yi zunubi. Amma in wani ya yi zunubi, muna da wani wanda yake magana da Uba don taimakonmu, wato, Yesu Kiristi, Mai Adalci.
2 He himself is the atoning sacrifice for our sins, and not ours only but also the whole world's. Shi ne hadayar kafara saboda zunubanmu, kuma ba don namu kaɗai ba amma har ma da zunuban duniya duka.
3 By this we know that we have come to know him: if we keep his commandments. Ta haka za mu tabbata cewa mun san shi in muna yin biyayya da umarnansa.
4 Whoever says, "I know him," yet doesn't keep his commands, is a liar—the truth isn't in him. Mutumin da ya ce, “Na san shi,” amma ba ya yin abin da ya umarta, maƙaryaci ne, gaskiya kuwa ba ta cikinsa.
5 But whoever keeps his word, the love of our Father is truly complete in him. This is how we know we are in him: Amma in wani ya yi biyayya da maganarsa, ƙaunar Allah ta zama cikakkiya ke nan a cikinsa. Ta haka muka san cewa muna cikinsa.
6 Whoever claims to remain in him ought to walk in the very way he walked. Duk wanda ya ce yana rayuwa a cikinsa dole yă yi tafiya kamar yadda Yesu ya yi.
7 Dear ones, I write you no new command, but an old one, held since the start—the old command is the word you heard. Abokaina ƙaunatattu, ba sabon umarni nake rubuta muku ba, a’a, daɗaɗɗen umarnin nan ne, wanda kuke da shi tun farko. Wannan tsohon umarni shi ne saƙon da kuka riga kuka ji.
8 Again, I write you a new command—true in him and in you—because the darkness is passing and the true light already shines. Duk da haka ina rubuta muku sabon umarni; ana ganin gaskiyar umarnin a cikinsa da kuma cikinku, gama duhu yana shuɗewa, haske na gaskiya kuwa yana haskakawa.
9 Anyone who says they're in the light but hates their brother or sister is in the dark even now. Duk wanda ya ce yana cikin haske yana kuma ƙin ɗan’uwansa, ashe a duhu yake har yanzu.
10 Whoever loves his brother or sister abides in the light, and in him there is no cause for stumbling. Duk wanda yake ƙaunar ɗan’uwansa, a cikin hasken yake rayuwa ke nan, kuma babu wani abin da yake cikinsa da zai sa yă yi tuntuɓe.
11 But whoever hates his brother or sister is in the dark, walking in the dark, not knowing where he's going—the dark has blinded his eyes. Amma duk wanda yake ƙin ɗan’uwansa, cikin duhu yake, yana kuma tafiya cikin duhu ke nan; bai ma san inda za shi ba, domin duhun ya makanta shi.
12 I write to you, little children, because your sins are forgiven for his name's sake. Ina rubuta muku, ’ya’yana ƙaunatattu, domin an gafarta muku zunubanku saboda sunansa.
13 I write to you, fathers, because you know the One from the beginning. I write to you, young men, because you have defeated the evil one. Ina rubuta muku, ubanni, domin kun san shi wanda yake tun farko. Ina rubuta muku, samari, domin kun ci nasara a kan mugun nan.
14 Children, I write because you know the Father. Fathers, I write because you know the One from the beginning. Young men, I write because you're strong, and our Father's word lives in you, and you've overcome the evil one. Ina rubuta muku, ’ya’yana ƙaunatattu, domin kun san Uba. Ina rubuta muku, ubanni, domin kun san shi wanda yake tun farko. Ina rubuta muku, samari, domin kuna da ƙarfi, maganar Allah kuwa tana zaune a cikinku, kun kuma ci nasara a kan mugun nan.
15 Do not love the world, or anything in the world. Whoever loves the world, the love of the Father is not in him. Kada ku ƙaunaci duniya, ko wani abin da yake cikinta. In wani yana ƙaunar duniya, ƙaunar Uba ba ta cikinsa.
16 Everything in the world—the craving of the flesh, the craving of the eyes, and the pride of life—is not from the Father but from the world. Gama duk abin da yake na duniya, kamar sha’awace-sha’awacen mutuntaka, sha’awar idanunsa, da kuma taƙama da abin da yake da shi, yake kuma yi, ba daga wurin Uba suke fitowa ba sai dai daga duniya.
17 The world and its cravings are passing away, but whoever does the will of our Father remains forever. Duniya da sha’awace-sha’awacenta suna shuɗewa, amma mutumin da yake aikata nufin Allah, zai rayu har abada.
18 Children, it is the last hour. As you heard antichrist comes, so now many antichrists have come; by this we know it's the last hour. ’Ya’yana ƙaunatattu, waɗannan su ne kwanakin ƙarshe; kuma kamar yadda kuka ji cewa magabcin Kiristi yana zuwa, ko yanzu ma abokan gāban Kiristi da yawa sun zo. Ta haka muka san cewa kwanakin ƙarshe sun iso.
19 They went out from us, but were not of us; if they had been of us, they would have stayed with us. But they left, to show that none of them belonged to us. Waɗannan masu gāba da Kiristi suna cikinmu a dā, amma sun bar mu, don tun dā ma su ba namu ba ne. Ai, da su namu ne, da har yanzu suna tare da mu. Amma sun bar mu, wannan ya nuna a fili cewa su ba namu ba ne.
20 But you have an anointing from the Holy One, and you all know the truth. Amma ku kam, kuna da shafewa daga wurin Mai Tsarkin nan, kuma dukanku kun san gaskiya.
21 I write to you not because you don't know the truth, but because you do—and no lie comes from the truth. Ina rubuta muku ba domin ba ku san gaskiya ba ne, a’a, sai dai domin kun santa, kun kuma san cewa babu yadda ƙarya za tă fito daga gaskiya.
22 Who is the liar, if not the one denying Jesus is the Christ? This is the antichrist, denying the Father and the Son. Wane ne maƙaryaci? Ai, shi ne mutumin da yake mūsun cewa Yesu shi ne Kiristi. Irin wannan mutum shi ne magabcin Kiristi, ya yi mūsun Uban da kuma Ɗan.
23 No one who denies the Son has the Father. Whoever confesses the Son has the Father also. Ba wanda yake mūsun Ɗan, sa’an nan yă ce yana da Uban; duk wanda ya yarda da Ɗan, yana da Uban a cikinsa ke nan.
24 You—let what you heard from the start remain in you. If what you heard from the start remains in you, you too will remain in the Son and the Father. Ku lura fa cewa abin da kuka ji daga farko, bari yă ci gaba da kasance a cikinku. In kuwa ya ci gaba da zama a cikinku, za ku kasance a cikin Ɗan, da kuma a cikin Uban.
25 And this is the promise that he himself made to us—eternal life. Wannan shi ne abin da ya yi mana alkawari, wato, rai madawwami.
26 I write these things to you about those who are trying to lead you astray. Ina rubuta muku waɗannan abubuwa ne game da waɗanda suke ƙoƙari su sa ku kauce.
27 As for you, the anointing you received from him remains in you, and you don't need anyone to teach you. But since his anointing teaches you about everything—true, not a lie—remain in him, just as it taught you. Game da ku kuwa, shafan nan da kuka karɓa daga gare shi tana nan a cikinku, ba kwa kuma bukata wani yă koyar da ku. Amma kamar yadda shafan nan tasa tana koya muku kome, ita kuwa gaskiya ce ba ƙarya ba, yadda dai ta koya muku, to, sai ku zauna a cikinsa.
28 And now, little children, remain in him, so that when he appears we may have confidence and not shrink from him in shame at his coming. Yanzu fa, ya ku ’ya’yana ƙaunatattu, sai ku ci gaba a cikinsa, domin sa’ad da ya bayyana, mu iya tsaya gabagadi babu kunya a dawowarsa.
29 If you know he's righteous, you also know that all who do right are born of him. In kun san cewa shi mai adalci ne, to, kun dai san cewa duk mai aikata abin da yake daidai haifaffensa ne.
FHB

Scripture from Father’s Heart Bible™. © 2026 Spirit Media Publishing, the imprint of Spirit Media Inc. All rights reserved. In Divine Voice™ Color, the words spoken by our Father show in blue, the words of the Son in red, and the words of the Spirit in purple.

OHCB

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible 2020 · Creative Commons - Attribution-ShareAlike [CC BY-SA]